Al'adun Gargajiya

Al'adun Gargajiya - Hallgatás Online

Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam.  Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.

00:00
00:00

Epizód összefoglalója

Shirin al’adun mu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan karon ya leka ƙasar Togo ne, inda muka yi ƙoƙarin jin yadda Hauasawan wannan ƙasa ke rayuwa. A Togo dai akwai kimanin Hasauwa dubu 30 da ke rayuwa da sauren ƙabilun wannan ƙasa ba tareda wata matsala, dai dai gwalgwado dangantaka na tafiya tsakanin su ba tareda an fuskanci wata matsala. Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Abdoulaye Issa................

Epizódok

402-

Yadda al'ummar Hausawa kusan dubu 30 ke rayuwa a tsakanin ƙabilun ƙasar Togo

Shirin al’adun mu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan karon ya leka ƙasar Togo ne, inda muka yi ƙoƙarin jin yadda Hauasawan wannan ƙasa ke rayuwa. A Togo dai akwai kimanin Hasauwa dubu 30 da ke rayuwa da sauren ƙabilun wannan ƙasa ba tareda wata matsala, dai dai gwalgwado dangantaka na tafiya tsakanin su ba tareda an fuskanci wata matsala. Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Abdoulaye Issa................

20 okt. 2026
401-

Bikin al'adun makiyaya na ƙasa a Jamhuriyar Nijar

'Al’adunmu Na Gado' na wannan mako tare da Nura Ado Suleiman ya sake yin tattaki ne zuwa garin Ingal da ke Yankin Agadez a Jamhuriyyar Nijar, inda aka gudanar da bikin ala’adu na ƙasa baki ɗaya da ke haɗa makiyaya daga ƙabilu daban-daban da ake yi wa laƙabi da 'Cure Salee'. An dai saba gudanar da bikin makiyayan ne a kowane makon farko na cikin watan Oktoba, da zummar ƙarfafa haɗin kai tsakanin makiyaya don zaman lafiya mai ɗorewa a tsakanin ƙabilu.

13 okt. 2026
400-

Mahukuntan Nijar sun karrama fitaccen mawaƙin gargajiya Mamman Gawo Filinge

Da yake mawaƙan gargajiya na da matuƙar tasiri a ƙasar Hausa, mahukunta sun karrama fitaccen mawaƙin Nijar, Marigayi Alhaji Mamman Gawo Filinge, inda aka raɗawa wani titi sunansa. Mawaƙin ya taka gagarumar rawa sakamakon waƙokinsa na siyasa da na gargajiya, da noma da kuma zamantakewa, lokacin da ya yi zamaninsa a shekarun 1960 zuwa 1980. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...

06 okt. 2026
399-

Jamhuriyar Nijar ta gudanar da bikin ranar Hausa ta bana a ƙasar

Shirin Al’adumu na gado a wannan makon ya sake waiwayar baukukuwan ranar Hausa ne ta Duniya, ranar da babban taronta ke gudana a dukkanin ranakun 26 ga watan Agusta duk shekara, to amma kasancewar bikin ya samu karɓuwa a gwamman ƙasashe ya sa bayan babban taron ake gudanar da wasu ƙarin bukukuwan ranar hausar ta Duniya a ƙasashe daban daban, ciki har da Jamhuriyar Nijar, inda aka gudanar da bikin zagayowar ranar hausar ta Duniya a ranar 8 ga watan Satumban da muke. Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Nura Ado Sulaiman.

15 szept. 2026
398-

Muhawara kan banbance tsakanin ƙabilun Hausawa da kuma Fulani a Najeriya

Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon ya mayar da hankali kan zamantakewa da auratayyar ƙabilun Hausawa da Fulani, ƙabilu 2 da suka juye zuwa Hausa Fulani bayan zaman tare na tsawon shekaru musamman a Najeriya. A baya-bayan nan muhawara ta fara zafi kan buƙatar banbance ƙabilun biyu zuwa Hausa daban da kuma Fulani zalla, lamarin da ya ci karo da fahimtar wasu daga cikin masana a ɓangaren al'adu. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

08 szept. 2026